Daga Umar Akilu Majeri, Dutse
Makarantar Sabil Rasheed Academy mai hedikwata a ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Jihar Jigawa, ta shirya walimar karramawa ga dalibai 22 da suka yi fice wajen haddar Alƙur’ani Mai Girma a matakai daban-daban.
An gudanar da walimar ne domin yabawa ƙwazo da jajircewar daliban, tare da ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da neman ilimin addinin Musulunci. Taron ya samu halartar iyaye, malamai da sauran baƙi a wani babban wurin taro da ke kusa da Limawa, kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Dutse.
Bayanan makarantar sun nuna cewa daga cikin daliban da aka karrama, akwai waɗanda suka haddace Alƙur’ani zuwa juzu’i 10 tare da tafsiri, wasu juzu’i 20, 30, 40 da 50, yayin da wasu kuma suka kammala haddar Alƙur’ani gaba ɗaya, wato juzu’i 60, tare da tafsiri da kuma tsattsafe.
Makarantar Sabil Rasheed Academy ta fara ne a Birnin Kudu, kafin daga bisani ta buɗe reshe a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa. Haka kuma, shugabannin makarantar sun bayyana cewa ana ci gaba da shirye-shiryen faɗaɗa ayyukanta zuwa Abuja domin ƙara bunƙasa harkokin ilimin addini a Najeriya.
Da yake jawabi, shugaban makarantar, Sheikh Sani Maje Sale, ya ce an shirya walimar ne domin zaburar da iyaye da dalibai kan muhimmancin haddar Alƙur’ani da neman ilimin addini.
Ya yi kira ga iyaye da su fifita koyar da ‘ya’yansu ilimin Alƙur’ani, yana mai jaddada cewa neman ilimin addini wajibi ne ga kowane Musulmi, domin ibada ba ta cika sai da ilimi.
Shehin malamin ya kuma gargadi iyaye da kada su riƙa barin son zuciyar ‘ya’yansu ya rinjayi tarbiyyarsu, yana mai cewa hakan kan haifar da nadama a nan gaba.
Haka kuma ya yabawa wani daga cikin daliban makarantar da ya haddace juzu’i bakwai na Alƙur’ani tare da tafsiri cikin shekara guda kacal, duk da nauyin karatunsa, yana mai cewa Allah Ya hore masa ƙwaƙwalwar haddace abin da aka koya masa cikin sauƙi.
Sheikh Sani Maje Sale ya ƙara da cewa makarantar ta samar da wani ingantaccen tsarin horas da mahaddata Alƙur’ani (Huffaz), wanda ake amfani da shi a dukkan rassan makarantar domin samar da malamai masu zurfin ilimin addini a Jihar Jigawa da ma Najeriya baki ɗaya.
Shi ma da yake nasa jawabin, Sheikh Mahamood Bashir, wanda ya taɓa lashe lambar zinare a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Sokoto, ya yabawa shugaban makarantar bisa ƙoƙarinsa na bunƙasa ilimin Alƙur’ani a Jigawa.
Ya bayyana cewa idan aka ci gaba da irin wannan ƙoƙari, Jigawa za ta kasance cikin jihohin da za su yi fice wajen samar da manyan malamai da mahaddatan Alƙur’ani a Najeriya.
Ya kuma buƙaci iyaye su halarci bikin bayar da takardun shaidar kammala karatu da makarantar za ta gudanar ranar Talata mai zuwa a babban dakin taro na Event Centre, yana mai cewa hakan zai ƙara wa dalibai ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da neman ilimi.













